Posts

SA MAZA GUDU Complete

 SAMAZA GUDU Littafi na daya Complet Littafin Abdulaziz sani madakin gini Part A A wani zamani can baya mai tsawo da ya shude a cikin daular larabawa a zamanin da babu wata huldar kasuwanci wacce tafi cinikin bayi, anyi wani babban birni mai suna Madinatul Zauwara. Birnin Madinatul Zauwara na karkashin mulkin wani gawurtaccen sarki ne ma'abocin jarumtaka, wanda ya zamo gwarzon mayaki kuma dodo ha dukkan sarakunan dake nahiyar, ana kiran wanna sarki da suna Sharkuf bin Aufan. Duk wani abu najin dadin duniya Allah yabawa sarki Sharkuf, yana da 'ya'ya guda tara amma dukkaninsu mazane, sai mace guda daya. Babban dansa kuwa shekararsa talatin da takwas, ana kiransa da Lahaman. Lahaman ya gado maifinsa a sadaukantaka da jarumta kuma shine yake jagorantakar dakarun sarki a duk sa'adda za'a fita FARAUTAR BAYI. A tarihin fitarsa farautar bayi sau sittin da uku  bai taba dawowa gida cikin rashin nasara ba, kuma duk sa'adda ya fita baya dawowa da kasa da bayi dubu uku, sau...